Hausa Bible
Matiyu 7
1 “Kada ku yanke wa kowa hukunci, domin kada a yanke muku.
2 Gama da irin shariˈar da kuke yi wa mutane, da ita za a yi muku shariˈa. Mudun da kuke auna wa mutane da shi, da shi za a auna muku.
3 Don me kake ganin ɗan tsinken da yake cikin idon ɗanˈuwanka, amma ba ka kula da gungumen da yake cikin idonka ba?
4 Ko kuma yaya za ka ce wa ɗanˈuwanka, ‘Bari in cire ɗan tsinken da yake cikin idonka,’ bayan gungume yana cikin naka idon?
5 Kai munafuki, ka cire gungumen da yake cikin idonka tukuna, domin ka iya gani sosai yadda za ka cire ɗan tsinken da yake cikin idon ɗanˈuwanka.
6 “Kada ku ba karnuka abu mai tsarki, kada kuma ku ba aladu luˈuluˈunku masu daraja. Gama za su tattaka, su kuma juya su yi muku ciwo.”
7 “Ku yi ta roƙo za a ba ku, ku yi ta nema za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa kuma za a buɗe muku.
8 Gama duk wanda ya roƙa za a ba shi, duk wanda ya nema zai samu, kuma duk wanda ya ƙwanƙwasa za a buɗe masa.
9 Ko akwai wani a cikinku, ku ubanni, wanda idan ɗansa ya roƙe shi burodi, sai ya ba shi dutse?
10 Ko kuma idan ɗan ya roƙe shi kifi, sai ya ba shi maciji?
11 Idan ku da kuke mugaye kun san yadda za ku ba ˈyaˈyanku abubuwa masu kyau, balle fa Ubanku na sama, ai, zai ba da abubuwa masu kyau ga waɗanda suka roƙe shi!
12 “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu, gama wannan shi ne manufar Koyarwar Musa da ta annabawa.”
13 “Ku shiga ta ƙaramar ƙofa, gama ƙofar zuwa halaka tana da fāɗi. Kuma hanyarta tana da sauƙin bi, masu shiga cikinta kuma suna da yawa.
14 Amma ƙofar zuwa rai, ƙarama ce. Hanyarta kuma da wuyar bi. Masu binta kuma ba su da yawa.”
15 “Ku yi hankali da annabawan ƙarya waɗanda suke zuwa wurinku da kamannin tumaki, amma a ciki su kyarketai ne masu tsananin yunwa.
16 Za ku gane su ta irin aikinsu. Za a iya samun ˈyaˈyan inabi daga jikin ƙaya? Ko kuwa a sami ɓaure daga jikin itacen ƙaya?
17 “Haka kuma kowane itace mai kyau yakan ba da ˈyaˈya masu kyau, itace marar kyau kuwa yakan ba da ˈyaˈya marar kyau.
18 Itace mai kyau ba zai iya ba da munanan ˈyaˈya ba, haka kuma mummunan itace ba zai iya ba da ˈyaˈya masu kyau ba.
19 Duk itacen da ba ya ba da ˈyaˈya masu kyau, sai a sare shi a jefar a cikin wuta.
20 Saboda haka, da irin aikin annabawan ƙaryar nan za ku gane su.
21 “Ba duk mai ce mini ‘Ubangiji, Ubangiji’ ne zai shiga mulkin sama ba. Sai dai wanda ya yi abin da Ubana wanda yake cikin sama yake so.
22 A Ranar nan mutane da yawa za su ce mini ‘Ubangiji, Ubangiji!’ ba mu yi waˈazi cikin sunanka ba? Ba mu kori aljanu cikin sunanka ba? Ba mu yi ayyukan ban mamaki da yawa cikin sunanka ba?
23 Saˈan nan zan ce musu, ‘Ni ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu yin mugunta.’
24 “Saboda haka duk wanda ya ji wannan magana tawa, ya kuma yi amfani da ita, zai zama kamar mai hikima wanda ya gina gidansa a kan dutse.
25 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi ambaliya, iska ta taso ta buga gidan, amma bai fāɗi ba, domin an gina shi a kan dutse ne.
26 “Duk wanda ya ji maganar nan tawa kuma ya ƙi ya aikata, zai zama kamar wani wawa wanda ya gina gidansa a kan yashi.
27 Da ruwa ya sauko, koguna suka yi ambaliya, iska ta taso ta buga gidan, sai gidan ya fāɗi, mummunar fāɗuwa kuwa.”
28 Da Yesu ya gama faɗa waɗannan abubuwan, sai taron mutanen suka yi mamakin koyarwarsa,
29 domin ya koya musu kamar mutumin da yake da iko, ba kamar malaman Koyarwar Musa ba.