Skip to content

Hausa Bible

Zabura 24

1 Duniya da dukan abin da yake cikinta na Ubangiji ne, Duniya da dukan mazaunanta nasa ne.

2 Ya gina ta a bisa ruwa mai zurfi na ƙarƙashin ƙasa, Ya kuma kafa harsashinta a zurfin teku.

3 Wa yake da iko yă hau tudun Ubangiji? Wa yake da iko ya shiga Haikalinsa tsattsarka?

4 Sai wanda yake da tsarki cikin aiki, da tunani, Wanda ba ya yi wa gumaka sujada, Ko kuma yă yi alkawarin ƙarya.

5 Ubangiji zai sa masa albarka, Allah Mai Cetonsa zai kuɓutar da shi.

6 Su ne irin mutanen da suke zuwa wurin Allah, Waɗanda suke zuwa a gaban Allah na Yakubu.

7 A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo!

8 Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji ne mai ƙarfi mai iko, Ubangiji mai nasara cikin yaƙi!

9 A buɗe ƙofofi sosai, A buɗe daɗaɗɗun ƙofofi, Babban Sarki kuwa zai shigo!

10 Wane ne wannan babban Sarki? Ubangiji Mai Runduna, shi ne babban Sarki!

Open Bible reader