Hausa Bible
Zabura 150
1 Yabo ya tabbata ga Ubangiji! Ku yabi Allah a cikin Haikalinsa! Ku yabi ƙarfinsa a sama!
2 Ku yabe shi saboda manyan abubuwa Waɗanda ya aikata! Ku yabi mafificin girmansa!
3 Ku yabe shi da kakaki! Ku yabe shi da garayu da molaye!
4 Ku yabe shi da bandiri kuna taka rawa! Ku yabe shi da garayu da sarewa!
5 Ku yabe shi da kuge! Ku yabe shi da kuge masu amo!
6 Ku yabi Ubangiji dukanku rayayyun talikai. Yabo ya tabbata ga Ubangiji!