Hausa Bible
Zabura 15
1 Wane ne zai iya zama cikin Haikalinka? Wa zai iya tsayawa a Sihiyona, wato tudunka tsattsarka?
2 Sai dai mutumin da yake biyayya ga Allah da kowane abu, Yana kuwa aikata abin da yake daidai, Wanda yake faɗar gaskiya da zuciya ɗaya,
3 Wanda kuma ba ya ɓāta sunan waɗansu. Ba ya zargin abokansa, Ba ya kuwa baza jita-jita a kan maƙwabtansa.
4 Yakan raina waɗanda Allah ya ƙi su, Amma yana girmama waɗanda suke yi wa Ubangiji biyayya, Kullum yana cika alkawaran da ya yi ko ta halin ƙaƙa,
5 Yana ba da rance ba ruwa, Ba ya karɓar hanci don ya yi shaidar zur a kan marar laifi. Wanda ya aikata waɗannan abubuwa ba zai taɓa fāɗuwa ba.