Skip to content

Hausa Bible

Zabura 138

1 Da zuciya ɗaya nake gode maka, ya Ubangiji, Ina raira waƙar yabonka a gaban alloli.

2 Na durƙusa a gaban tsattsarkan Haikalinka Ina yabon sunanka. Sabili da madawwamiyar ƙaunarka da amincinka, Saboda ka nuna ɗaukakarka da umarnanka.

3 Ka amsa mini sa'ad da na yi kira gare ka, Da ƙarfinka ka ƙarfafa ni.

4 Dukan sarakunan duniyar nan za su yabe ka, ya Ubangiji, Gama sun riga sun ji alkawaranka.

5 Za su raira waƙa a kan abin da Ubangiji ya yi, Za su raira waƙa kuma a kan ɗaukakarsa mai girma.

6 Ko da yake Ubangiji yana can Sama, Duk da haka yana kulawa da masu kaɗaici. Masu girmankai kuwa ba za su iya ɓoye kansu daga gare shi ba.

7 Ko lokacin da nake tsakiyar wahala, Za ka kiyaye ni lafiya, Ka yi gāba da abokan gābana, waɗanda suka husata, Za ka kuwa cece ni da ikonka.

8 Za ka aikata kowane abu da ka alkawarta mini, Ya Ubangiji, ƙaunarka madawwamiya ce har abada. Ka cikasa aikin da ka fara.

Open Bible reader