Skip to content

Hausa Bible

Zabura 133

1 Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!

2 Yana kama da man zaitun mai daraja, Wanda yake naso daga bisa kan Haruna zuwa gemunsa, Har zuwa wuyan riganunsa.

3 Kamar raɓa a bisa Dutsen Harmon, Wadda take zubowa a bisa tuddan Sihiyona. A can ne Ubangiji ya alkawarta albarkarsa, Rai na har abada.

Open Bible reader