Hausa Bible
Zabura 128
1 Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa!
2 Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka, Za ka yi farin ciki ka arzuta.
3 Matarka za ta zama kamar kurangar inabi Mai 'ya'ya a gidanka, 'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitun Suna kewaye da teburinka.
4 Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya, Hakika za a sa masa albarka kamar haka.
5 Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona! Ya sa ka ga Urushalima ta arzuta Dukan kwanakinka!
6 Ya kuma sa ka ka ga jikokinka! Salama ta kasance ga Isra'ila!