Hausa Bible
Zabura 125
1 Waɗanda suke dogara ga Ubangiji, Suna kama da Dutsen Sihiyona, Wanda ba zai jijjigu ba, faufau. Faufau kuma ba za a kawar da shi ba.
2 Kamar yadda duwatsu suka kewaye Urushalima, Haka nan Ubangiji zai kewaye jama'arsa, Daga yanzu har abada.
3 Ba a koyaushe mugaye za su yi mulki a ƙasar jama'ar Allah ba, Idan kuwa suka yi, to, ya yiwu jama'ar Allah s u yi laifi.
4 Ya Ubangiji, ka yi wa mutanen kirki alheri, Su waɗanda suke biyayya da umarnanka!
5 Amma ka hukunta waɗanda suke bin mugayen al'amuransu, Sa'ad da kake hukunta wa masu aikata mugunta! Salama ta kasance tare da Isra'ila!