Hausa Bible
Zabura 123
1 Ya Ubangiji, ina zuba ido gare ka, A Sama inda kake mulki.
2 Kamar yadda bara yake dogara ga maigidansa, Baranya kuma ga uwargijiyarta, Haka nan muke zuba ido gare ka, ya Ubangiji Allahnmu, Har mu sami jinƙanka.
3 Ka yi mana jinƙai, ya Ubangiji, ka yi mana jinƙai, An gwada mana wulakanci matuƙa!
4 Attajirai sun daɗe suna ta yi mana ba'a, Azzalumai masu girmankai sun raina mu!