Skip to content

Hausa Bible

Zabura 1

1 Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah.

2 Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana.

3 Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi.

4 Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.

5 Allah kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai.

6 Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse.

Open Bible reader