Hausa Bible
Ayuba 25
1 Bildad ya amsa.
2 “Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa, A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama.
3 Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima? Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba?
4 Akwai wanda ya isa ya zama adali, Ko mai tsarki a gaban Allah?
5 Hasken wata ba haske ba ne a gare shi, Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.
6 To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah?”